Posts

Showing posts from June, 2017

Budar dawa

SASHEN HARSUNAN NAJERIYA JAMI’AR UMARU MUSA YAR’ADUA KATSINA KWAS: NLH 2206 HAUSA DRAMA (WASAN KWAIKWAYO NA HAUSA) TAMBAYA ME AKE NUFI DA WASAN BUXAR DAWA? YA AKE AIWATAR DASHI, SUWA SUKE YINSA, KUMA DON ME, SHIN YANA DA WANI TASIRI GA HAUSAWA, MINENE ALAQAR SA DA WASAN KWAIKWAYO? DAGA XALIBAI KAMAR HAKA SN SUNA LAMBA 1 BISHIR IBRAHIM MASANAWA U1/14/NLH/1076 2 YUSUF SULAIMAN UMAR U1/11/ISL/0765 3 IBRAHIM MUHAMMAD MUHAMMAD U1/14/NLH/2014 4 AYUBA IBRAHIM M U1/13/NLH/1284 5 HARUNA SAGIR KAKEYI U1/14/NLH/2049 TSAKURE Wasan kwaikwayo kamar su wasan tashe da wasan takai da wasan wowo da wasan kalankuwa da buxar dawa, da shan kabewa da sauransu, Kamar yadda sunan su ya nuna asalinsu duk daga wasan kwaikwayo ne. Don haka wannan takarda za ta bi diddiqi ne akan wasan kwaikwayo da buxar dawa.   GABATARWA  Manufar wannan takarda ita ce ta tantance dangane da wasan buxar dawa, dangane da yanda ake aiwatar dashi tare da fexe shi a gane...