Budar dawa
SASHEN HARSUNAN NAJERIYA
JAMI’AR UMARU MUSA YAR’ADUA KATSINA
KWAS: NLH 2206 HAUSA DRAMA (WASAN KWAIKWAYO NA HAUSA)
TAMBAYA
ME AKE NUFI DA WASAN BUXAR DAWA? YA AKE AIWATAR DASHI, SUWA SUKE YINSA, KUMA DON ME, SHIN YANA DA WANI TASIRI GA HAUSAWA, MINENE ALAQAR SA DA WASAN KWAIKWAYO?
DAGA XALIBAI KAMAR HAKA
SN
SUNA
LAMBA
1
BISHIR IBRAHIM MASANAWA
U1/14/NLH/1076
2
YUSUF SULAIMAN UMAR
U1/11/ISL/0765
3
IBRAHIM MUHAMMAD MUHAMMAD
U1/14/NLH/2014
4
AYUBA IBRAHIM M
U1/13/NLH/1284
5
HARUNA SAGIR KAKEYI
U1/14/NLH/2049
TSAKURE
Wasan kwaikwayo kamar su wasan tashe da wasan takai da wasan wowo da wasan kalankuwa da buxar dawa, da shan kabewa da sauransu, Kamar yadda sunan su ya nuna asalinsu duk daga wasan kwaikwayo ne. Don haka wannan takarda za ta bi diddiqi ne akan wasan kwaikwayo da buxar dawa.
GABATARWA
Manufar wannan takarda ita ce ta tantance dangane da wasan buxar dawa, dangane da yanda ake aiwatar dashi tare da fexe shi a gane shin wasan kwaikwayo ne,
Wasan kwaikwayo na dandali wasa ne da aka gada daga iyaye da kakanni domin nishadi da kuma faxakar da juna dangane da rayuwar yau da gobe ke tafiya acikin al’umma. Wasan kwaikwayo ko da ji sunan sa ya riga ya bayyana kansa wato akwai alamun wasa, abinda yake raha, akwai kuma alamun kwaikwayo , wato aikata wani abu don kwatanta yadda ake yin sa,don wani ya gani ko waxansu su gani su gane kyansa ko muninsa. Wannan ma’ana ta na da alaqa da ma’anar drama ko (play) sunan da turawa suka ba wasan kwaikwayo domin kalmar drama ko (play) na nuni da aikata wani abu musamman a dandamali ko dandali domi n ya sa nishaxi ga masu kallon sa ko ya xaga masu hankali don su koyi wani abu. Sunan da Hausawa suka ba abinda turawa su ke kira drama wato wasan kwaikwayo ya bada damar a fahimci sigarsa da amfaninsa ta sigogi da dama. Hausawa sun yi amfani da kalmar nan “kwaikwayo” wadda ita ce ginshiqin hanyoyin da xan Adam ya ke bi ya na koyon magana,sarrafa harshe da sauransu. Saboda haka kusan a kowane abu a kanemi kwaikwayo sai ka ga wani rukuni ne guda a cikin rayuwa.
Ta hasken wannan bayani na wasan kwaikwayo zamu iya leqawa mu ga ire-iren sa kamar yadda yake a cikin Hausawa, yaransu da manyansu, kuma mu fahimci cewa wasan kwaikwayo daxaxxar al’ada ce a cikin rayuwar Hausawa. Ganin yadda aka bayyana ma’anar wasan kwaikwayo zamu iya cewa akwai al’adu da dama waxanda suka danganci wasan kwaikwayo a cikin Hausawa. Su waxannan al’adu akwai waxanda yara ko samari su ke kwaikwayo tsakaninsu,wannan shi ake kira wasan kwaikwayo na asali ko gargajiya misali
Ire-iren wasan kwaikwayo ya haxa da:-
Wasan langa,Wasan Xan Akuyana,‘Yartsana,Wasan tashe.
Bayan irin waxannan wasannin na gargajiya na yara da samari wato akwai waxansu al’adu da manya su kanyi masu siffar wasan kwaikwayo. A cikin irin waxannan al’adu akwai:-
Bori ,Dabo-dabo,Kalankuwa,Wowo,Bikin shan kabewa,Bikin buxar dawa.
Amma dangane da yadda zamani ke tafiya, wasan na canzawa tare da rikixewa zuwa al’adar wata al’umma sabanin ta Hausawa kuma wannan wata barazana ce ga cigaban al’adun hausawa. Amma duk da haka dakwai waxanda ke qoqarin farfaxo da wasannin kwaikwayo.
Haka nan wasu masana sun qara bada haske ga me da ma’anar wasan kwaikwayo. Ga kaxan daga cikinsu:
Yar’adua (2008) ya bayyana wasan kwaikwayo da cewa wata hanyace tabaje kolin halayen jama’a da yanayin rayuwarsu ta cikin nishaxi da raha domin su gani su kuma zavi nagari suyi amfani da su,suyi watsi da munanan domin su gyara rayuwarsu.
Da fatan kayan cikin wannan takarda zai warware bakin zaren dukkanin hasashe-hasashen mai hasashe.
Ma’anar wasan kwaikwayo
Ta fuskar ma’ana wasan kwaikwayo na da bangare biyu: wasa da kwaikwayo, kamar yadda Xangambo (2008:25) ya bayyana shi wasan ko wasa na iya daukar abinda ba dagaske ba ko kishiyar kalmar wato ba faxa ba. Kamar yadda Hausawa kan ce idan abu ba faxa bane sai ace “wasa ne”. amma xayan vangaren ana iya siffanta kalmar da wani yanayi na holewa ko nishaxantarwa ko motsa jiki. Ita kalmar kwaikwayo kuwa za’a iya cewa tana nufin “koyi” da wani abu , misali kwaikwayon hawan sallah da yara qanana da kanyi a yau, suna kokarin kwatanta hawan sallah na ainihi wanda akeyi a kasashen Hausawa a lokacin bikin sallah qarama ko babba, a inda yaran kan sami kara su kwatanta shi da doki ,sannan su zavi xaya daga cikin su ya zame kamar sarki.
Kenan wasan kwaikwayo qoqari ne na kwatanta wasu halaye ko xabi’u ko ayyuka na wasu mutane ko al’adu domin a nishaxantar da al’umma ko ilimantar da ita ko a gargaxeta.
Alal haqiqa masana sun qari juna domin ganin sun fito da wannan ma’ana ta wasan kwaikwayo misali
Xangambo (2008:25) yana mai ra’ayin cewa kwaikwayo wasa ne da aka ginashi kan kwaikwayon wani labari, ko wata matsala ta rayuwa da ake son nusarwa ga jama’a. akan aiwatar da labarin,matsalar da sauransu cikin siffar “yaqini” wato “zahir”. Ba shakka shaihun malamin namu yafito mana da muhimman sassa guda biyu cikin wannan ma’ana, da farko ginuwar wasan kwaikawayo akan wani labari kowata matsala. Abu na biyu yadda ake aiwatar da labarin ko matsalar cewa a siffar yaqini ne take, wato zahiri.
‘Yar’adua (2007:1) ya dubi wasan kwaikwayo kamar haka “ginshiqin rayuwar al’umma ne,saboda ta hanyarsa ce mutum yake koyon yadda zai rayu,domin da kwaikwayo ne mutum yake koyon abubuwan rayuwarsa. Masana ilimin halayyar xan Adam sun tabbatar da cewa hanyar farko ta koyon rayuwa ita ce kwaikwayo “bako tantama malamin ya nuna gabaxayan rayuwa naginuwa ne bisa kwaikwayo, domin ya fito da abinda yake gaskiya a rayuwa ta zahiri,saboda hanyar farko ta koyon rayuwar xan Adam ita ce kwaikwayo, wadda zai ci gaba da ita hartsufansa.Shi kuwa:-
Ahmad (2007) dubar ma’anar yai ta hanyar fuska biyu wato duk wata matsalar wasa ta qunshi abu biyu; na farko ta kasance wasa ne ko kuma abu ne wanda ba da gaskiya ba lokacin da yin abin, na biyu shi ne wasan ya zama maqasudin na sake kama ne. amma wajen sake kamar nan in ji malamin, mai wasan, ko “yan wasan zasu canza kamannin su na yau da kullum. Mai yiwuwa ma sake kamar nan zai iya zama ta sigar tufafin yan wasan ne ko abubuwan da suke amfani dasu ko abubuwan da suke yi. Haka ne, wannan ko shakka babu, dole ne wasan kwaikwayo ya kasance ba dagaske ba ne, duk da cewar ana son aiwatar da shi ta fuskar yaqini kuma ya xauki salon sauya kamanni daga “yan wasan ko abinda ake son aiwatarwa xin, akasin haka kuwa to, ba wasan kwaikwayo za’a yi ba. Domin wasan kwaikwayo tamkar madubi ne na hoton al’ummar da ake son a kwaikwaya.
A ra’ayin Umar (1987:46) cewa yayi wasan kwaikwayo a adabin baka shi ne kamancen da, bayan an shirya shi, aka gabatar a aikace, ta hanyar zancen baki . misalin irin wannan kamance a Hausa, sun haxa da wasan “yartsana da tashe da “yan kamanci da hoto da bori”. Lallai malamin yayi magana domin shi kansa wasan kwaikwayo yana qarqashin adabi ne, wanda ya kasu gida biyu wato adabin baka na (gargajiya) da (rubutacce). Ire-iren hikimomi da fasahohin da ke cikin adabin baka sun qunshi wasan kwaikwayo; saboda hikimar shirya shi a ka take, sannan ana aiwatar da shi a zahiri.
A ra’ayin Alkanci (1990) kuwa wasan kwaikwayo shi ne tsarin koyar da jama’a waxansu halayen zaman duniya da ake son lura da su da su acikin tsanaki, amma a aikace cikin nishaxi da annashuwa. Wannan ra’ayin ya kusan dai-dai da na,
Xanjuma (2004) a kan ma’anar wasn kwaikwayo , cewa hanya ce ta ilimantarwa da faxakarwa da kuma nishaxantarwa.
A ra’ayin mu muna ganin wasan kwaikwayo wata hanya ce ta nuni da kyawawan halaye ko dabi’u da a ake fadakar da jama’a cikin nishaxi wato a hikimance.
2.1 BUXAR DAWA
Wasan Buxar dawa buki ne da Hausawa kanyi shekara-shekara don neman tsari daga cututtukan shekara da kuma sanin abinda shekarar zata kawo. Bokaye da Maharba da Manoma su suke shugabantar wannan buki. Anayin wannan buki ne bayan ruwan damana ya xauke da wata huxu.idan wannan wata na huxu ya kama ranan sha huxu ake gudanar da wannan wasa.
- Ya ake aiwatar da shi?
- Suwa ke yin sa?
- kuma don me?
- Shin ya na da tasiri ga Hausawa?
- Minene alaqar sa da wasan kwaikwaiyo?
Za muyi bayani xaya bayan xaya.
2.0.1 YADDA AKE AIWATAR DA SHI
Yanda ake aiwatar da shi wannan wasa na Buxar dawa shi ne dazarar damina ta kau, bayan wata huxu (sha huxu ga wata) akeyin wannan wasa (buki), tun kafin lokacin za’a sana’ar da mutanen gari da na kauyuka, wato dai ana karaxe gari ne da shela tare faxin ranar da za’ayi. Haka zalika za’a fitar da qauyen da za’a gudanar da wasan tare da dajin da za’a aiwatar.
Waxanda kuwa su ke lissafin watannin xaukewar ruwa da ranakun wata sukan san ranar tun kafin tazo. Tun kafin ranar jama’a zasu yi ta taruwa a garin da za’ayi Buxar dawar, idan ana gobe za’ayi wasan (bukin), da la’asar sai manyan Manoma da Bokaye da Maharba a karkashin shugabancin babbansu su fita su kewaye dajin da za’a yi farauta a cikinsa.
A ranar da za’ayi wasan(bukin) da sassafe sai manya da sauran jama’a tare da kaxe-kaxe da bushe-bushe zasu ta samma dajin domin yin farauta. Idan an fita duk dabbar da aka fara cin karo da ita sai a kashe a kawo a gaban manya, Bayan nan sun yi al’adar da za su yi sai susa a fexe dabbar da aka yo farautar a gaban jama’a, da zaran an fexe sai a fito da tumbinta sai manyan su zauna nazarin kayan cikin tumbin don su gane abinda zai faru a shekarar a dalilin dubiya da zasuyi ma tumbin da nazarin sa. Idan sun sami qwari ko tsutsotsi a cikin tumbin sai su lura idan qwarin nan matattu sun fi ya wa sai su ce a shekara mai zuwa za’ai mace-mace. Idan kuwa qwarin ba matattu ba ne amma duk ba su da kuzari kamar mai lafiya sai su ba da labari shekara mai zuwa za’ayi cuce-cuce (cututtuka) amma ba mutuwa da yawa. Idan kuwa suka tarar da tumbin akwai ruwa da yawa a cikinsa sai afaxa musu cewa wannan shekarar za’a samu ruwa dayawa, idan ya kasance a katarar tumbin baruwa sosai sai su ba da labarin a shekarar za’ayi fari. Wannan shi ne misali kadan da ga cikin irin abubuwan da su ke faxa.
Bayan angama karanta abinda ke cikin tumbin, sai kuma a shiga rabon naman zuwa qungiyoyin mutane. Kowa zai kokarin ya sami naman dabbar nan kome kankantarsa, wanda ya sami naman sai yakai gida a saka cikin girkin abincin gidan sa. Irin wannan abinci idan angama ana raba ma dangi kowa ya samu ya ci, sun ce cin irin wannan abinci da akeyi da wannan nama zai tsare wanda yaci daga sharrin cuce-cuce (cututtuka) da masifun wannan shekara,irin wannan wasa (buki) yayi sauqi bayan zuwan musulunci amma haryanzu anayin sa a birnin Qwanni cikin jamhuriyar Niger.
2.0.2 SUWA SU KE YINSA
Dan gane da mutanen da ke aiwatar da wasan (buki) Buxar dawa kuwa kamar yanda bayani ya gaba ta mun ga cewa Manoma ne da Mafarauta tare da Bokaye ke aiwatar da shi. Sana mutanen gari su mara masu baya domin aiwatar da Buxar dawa.
2.0.3 KUMA DON ME AKE YIN SA
Dalilin da yasa ake gudanar da wasan Buxar dawa (buki) shi ne kamar haka:
Don kariya ga al’ummar gari
Don ri ga kafin cututtuka
Don tattalin arzikin qasa
Don karin hadin kai tsakanin al’umma
2.0.4 TASIRIN SA GA HAUSAWA
Alal haqiqa wasan buxar dawa tasirin sa ga Hausawa a bayyane yake domin kuwa tun tali-tali ansan Bahaushe da farauta da noma, hakan yasa muke ganin lallai budar dawa tayi tasiri a cikin Hausawa. Sai dai a lokacin Bahaushe yana Bahaushen sa kafin ya samu harafi biyar wato Malam + Bahaushe =Malam Bahaushe. A taqaice dai bayan musulunci ya riske shi.
2.0.5 ALAQAR SA DA WASAN KWAIKWAYO
Kamar dai yadda muka gani Wasan Buxar dawa wasa ne (buki) ne da Hausawa kanyi shekara-shekara don neman tsari daga cututtukan shekara da kuma sanin abinda shekarar zata kawo. Bokaye da Maharba da Manoma su suke shugaban tar wannan buki. Anayin wannan buki ne bayan ruwan damana ya xauke da wata huxu.idan wannan wata na huxu ya kama ranan sha huxu ake gudanar da wannan wasa.
Shi kuma wasan Kwaikwayo hanyace tabaje kolin Al’umma wanda ya haxa da fito da Al’adunsu,tufafinsu,abincin su, kana a dayan vangare tasa nishaxi, wani sa’ilin ya sa masu karsashi,kana fito da kyawawan xabi’u ko akasin haka domin yin koyi. Haka zalika muhalli, lokaci muhimman abubuwa ne ga wasan kwaikwayo.kana ta fuskar kwaikwayon zamu ga cewa bokaye kan kwaikwayi halaye da xabi’u na aljannu su aiwatar da shi a wurin bukin buxar dawa kamar yadda wasan kwaikwayo kan kwaikwayi xabi’u na halayyar mutane na asali, kana idan aljanin kuturu ne anan zai dinga nuna hotonsa irin na kutare ma’ana alokacin aljanin da ke kansa kuturu ne.
Ka na ta fuskar wasa da kwai kixa da bushe-bushe da raye-raye akan aiwatar a wajen bikin buxar dawa abin lura anan wasan kwaikwayo da ake yi adandamali shi ma ana aiwatar dashi da kixe-kixe da bushe-bushe da raye-raye a yayin aiwatar da shi.
Idan mukayi la’akari da wannan bayani zamu ga cewa wasan buxar dawa ya na da alaqa da wasan kwaikwayo sabili da wasan kwaikwayo hanyace ta fito da al’adu,haka zalika za mu ga cewa wasan Buxar dawa hanyace itama da Hausawa suke nuna al’adunsu da sana’o’insu.
KAMMALAWA
Wannan bincike ya sami nasarar cimma qudirinsa na bincike ga me da Buxar dawa ,tareda yin tsokaci dangane da alakarsa da wasan Kwaikwayo. A qarshe an fito da dalilan da suke sa wa ayi Buxar dawa da kuma amfaninsa ga al’ummar Hausawa. Qarshe muna fatan kwalliya ta biya kuxin sabulu bincike a wannan bincike. Alhamdulillahi
MANAZARTA
A.M. Bunza (2004) Gwagwarmayar malam mai katuru da malaman kasar Hausa Takardar da aka gabatar a taron (karawa juna sani) a bukukuwan shekara (200) da kafa daular Musulunci ta sakkwato
M.S Ibrahim (1982) Dangantakar Al’ada da Addini,Tasirin Musulunci kan rayuwar Hausawa ta gargajiya. Kundin digiri na Biyu da aka gabatar a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua
I.A Banki (2010) Matsayin fashi a qagaggun labarun Hausa. Kundin digiri na biyu da aka gabatar a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria
A.Xanmaigoro (2013) Rubutaccen wasan kwaikwayo na Hausa Nazarinsa,Sigoginsa ta madubin ra’o’in zahiranci, siga da aiwatarwa
C.H. Robinson (1913) Dictionaryof Hausa Language third edition

Ina son na san yadda ake yin bukin budar dawa
ReplyDeleteDa kyau
ReplyDeleteAllah ya ƙara wa ilimi albarka

ReplyDeleteAllah ya saka da alkhairi ya kara basira da Sanya Hausa cikin haruna mafiya girma a duniya
ReplyDelete